Ya zuwa ranar Juma'a 9 ga watan nan, alkaluman kididdiga na nuna cewa mutane 20,972 ne suka harbu da cutar Ebola a duniya baki daya, inda cikin su 8,259 tuni suka riga mu gidan gaskiya.
Game da karin matakan da ake dauka domin shawo kan yaduwar cutar, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta ce za a yi aikin gwajin allurar rigakafin cutar ta Ebola guda biyu kan Bil Adam.
Shugaban babban taron tattaunawa kan allurar rigakafin cutar Ebola, da tattara kudade, kuma farfesa a jami'ar Witwatersrand dake kasar Afrika ta kudu Helen Rees, ya ce ya zuwa yanzu, babu wata allurar rigakafi dake iya hana kamuwa da cutar Ebola. Sai dai kamfanonin samar da alluran rigakafi, da hukumomin nazarin alluran, da dai sauran hukumomin lafiya za su yi aikin gwajin wasu alluran rigakafi biyu kan Bil Adam, alluran da ake sa ran za su yi amfani.
Helen Rees ya ce ganin yadda cutar Ebola ta yi matukar yaduwa a wannan karo, hukumomin hada magunguna za su yi kokarin fitar da allurar rigakafi masu nagarta. (Amina)