Kwanan baya, hukumar kiwon lafiyar duniya wato WHO ta sanar da cewa, ta amince da wani sinadarin da ke tabbatar da kamuwa da cutar Ebola da wani kamfanin kasar Sin ya kera, sa'an nan ta shigar da shi cikin takardar jerin sunayen magungunan da za ta saya. Har wa yau kuma ta gabatar da wannan sinadari kirar kasar Sin ga kasashen duniya don amfani da shi a fannin tabbatar da kamuwa da cutar ta Ebola.
Kafin wannan kuma, wannan sinadari ya samu amincewa daga gwamnatin kasar Sin da kuma kungiyar tarayyar Turai wato EU.
Gabatar da wannan sinadari kirar kasar Sin a duniya da hukumar WHO ta yi, ya kasance wata gudummowa da kasar Sin ke bayarwa wajen yaki da cutar Ebola a fadin duniya. (Tasallah Yuan)