in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ta yiwu jemagu ne ke yada Ebola tsakanin mutane
2014-12-31 10:58:33 cri

Wani bincike na nuni da cewar, jemagu suke yada cutar Ebola a tsakanin mutane a Afrika ta yamma.

Wasu masu bincike daga cibiyar Robert Koch ta Berlin dake kasar Jamus ta ce, alkalumma na nuni da cewar, tsuntsaye jemagu da alamu suna da hannu wajen yada kwayar cutar Ebola a Afrika ta yamma, kuma a bisa dukkan alamu, hakan ya faru ne a yayin da jemagun suka samu alaka da 'yan adam.

Rahoton wanda aka buga a wata mujalla ta magunguna ta yi nuni da cewar, namun daji ba su da hannnu wajen yada cutar, kuma tsuntsaye jemagu su ne ke haddasa wannan ta'asa da ta haddasa asaran rayukan jama'a da dama, musamman a Afrika ta yamma.

Masu bincike da suka fito daga bangarori dabam-dabam sun aiwatar da wani bincike na makonni 4 a kasar Guinea a watan Aprilu, domin tantance hulda tsakanin jemagu da mutane, da kuma duba rayuwar namun daji.

Masu binciken sun kuma kame wadansu jemagun a garin Meliandou da kuma wasu gandun dajin dake kusa, inda suka kaddamar da gwaji a kan tsuntsayen domin gano gaskiyar yadda cutar ta Ebola ke yaduwa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China