Shugaba Francois Hollande na kasar Faransa ya yaba da sakamako mai gamsarwa na maganin gwajin cutar Ebola da kwararrun kasar ta Faransa suka gudanar a kasar Guinea
Wata sanarwa da shugaban na Faransa ya bayar ta ce, sakamakon gwajin maganin abin karfafa gwiwa ne, ganin yadda ake samun raguwar mutuwar mutanen da ke dauke da cutar.
A watan Disamban shekarar da ta gabata ce, cibiyar binciken lafiya ta kasar Faransa (INSERM) tare da taimakon hukumomin kasar Guinea, kungiyar likitoci ta na gari na kowa (MSF) da kungiyar Alima mai zaman kanta, kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta kasar Faransa suka gudanar da gwajin farko na maganin da kamfanin harhada magunguna kasar Japan mai suna Toyama ya samar a Guinea Conakry don tantance sahihancinsa.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa, tun lokacin da cutar Ebola ta barke a watan Maris na shekara 2014, cutar ta halaka mutane 8,500 a kasashen Guinea, Liberia, Najeriya da Saliyo. (Ibrahim)