Kudurorin dai sun shafi batutuwan masu alaka da magance yaduwar ciwon hanta, da batun shawo-kan cututtuka marasa yaduwa da sauran su. Kaza lika an zartas da kudurori biyu da suka shafi "Manyan tsare-tsaren likitancin gargajiya, daga shekarar 2014 zuwa ta 2023", wanda kasar Sin da sauran kasashen duniya da dama suka yi hadin gwiwar gabatarwa.
Yayin dai wannan taro, an mai da hankali matuka kan shawarwarin bunkasa sha'anin kiwon lafiya a duniya, bayan shekarar 2015. Inda aka shafe kwanaki 6 kafin zartas da shirin ayyukan kulawa da nakasassu na duniya, da shirin ayyukan kulawa da kiwon lafiya dalafiyar tunani, da babban tsarin likitancin gargajiya da sauran batutuwa na shekaru da dama masu zuwa.
Bugu da kari, game da manyan matsalolin da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya a yanzu kuma, taron ya zartas da kudurorin shawo kan cututtuka marasa yaduwa, da yaki da raguwar amfanin magunguna da sauransu.
Babbar sakatariyar hukumar WHO Margaret Chan ta bayyana cewa, wakilai kimanin 350 daga bangarori daban daban ne suka halarci wannan babban taro, inda yawa-yawan batutuwan da aka tattauna, da yawan bayanai da kudurori da aka gabatar suka wuce na baya. A cewar ta hakan ya bayyana cewa, yawan matsalolin kiwon lafiya na karuwa a duniya, a hannu guda kuma ana miada hankali matuka ga batun tinkarar irin wadannan kalubaloli.(Fatimah)