A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu baya ga wasu da dama da suka jikkata, sakamakon fashewar wani bom, da aka dana a cikin wata mota a birnin Maiduguri na jihar Borno dake tarayyar Najeriya.
Wani ma'aikacin ceto ya shaidawa manema labaru cewa, da misalin karfe 8 da mintoci 10 na safe ne bam din ya tashi a kasuwar dake ci a ranar Litinin. Kuma ko da yake a ranar Talata ne, duk da hakan akwai mutane da dama a kasuwar lokacin da wannan lamari ya auku.
Ya zuwa yanzu dai, babu wata kungiya ko daidaikun mutane da suka dauki alhakin aiwatar da harin.
Jihar Borno dai ita ce sansanin kungiya masu tsattsauran ra'ayi ta Boko Haram, wadda ta sha kaddamar da hare-hare a sassan arewacin Najeriya. (Amina)