Rahotanni jami'an tsaro da masu gudanar da aikin ceto, sun ce an jefa bam din ne a yayin da jama'a ke kallon kwallo kwallo.
'Yan sanda da masu aikin ceto sun shaidawa kamfanin dillanci labarai na Xinhua cewar babu cikakken bayanin yawan mutanen da suka mutu, amma jami'ai sun bada tabbacin cewar an kwashi gawawwakin mutane da dama.
Ya kuma ce da misalin karfe shida na yamma ne ran Lahadi bam din ya tashi.
Kawo zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki nauyin kai wannan harin, to amma 'yan sanda sun ce ta yiwu kungiyar nan mai tsautsauran ra'ayi ta Boko Haram na da hannu a cikin harin da aka kai. (Suwaiba)