Wata tawagar hadin gwiwa a karkashin jagorancin gwamnatin Najeiya, HCR, PAM da wasu kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu da ta isa garuruwa biyu dake yankin tafkin Chadi a farkon watan Mayu ta gano 'yan Najeriya dake gudun hajira 1077 daga cikin iyalai 285 da suka gudu daga Najeriya dalilin tashe tashen hankali da na ayyukan keta hakkin dan Adam. Haka kuma tawagar ta kididdige 'yan asalin Chadi 361 daga cikin iyalai 55 da suka baro Najeriya. Hukumar HCR da abokan huldarta sun taimakwa 'yan gudun hijirar Najeriya da na Chadi da kayayyakin bukatun yau da kullum. Haka kuma da wasu sauran 'yan gudun hijira da wadanda aka kwashe da ma 'yan asalin sauran kasashe kamar Mali, na iyar kasancewa cikin wannan yankin, ko da yake zuwa wannan wuri na da matukar wuya, in ji mista Dian Balde.
A cewar jami'in na HCR, yawancin mutanen da suka isa Chadi daga su sai tufafi kuma suna cin abinci sau daya a jini. Suna bukatar abinci, ruwan sha, mazugunni, tsafta da kiwon lafiya. (Maman Ada)