An gudanar da bikin gabatar da takardar ne a fadar gwamnatin Kano.
Bikin wanda ya samu halartar hakimai da manyan `yan majalissar Sarki da kuma `wasu daga cikin `ya yan marigayi Alhaji Ado Bayero, ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Jim kadan da sanya hannu kan takardar rantsuwar, sabon sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi ya yi alkawarin gudanar da aiki ba tare da nuna son zuciya ba, kuma zai rungumi kowa da kowa cikin adalci.
Ya tabbatar da cewa dukkannin al`ummar dake rike da masarautar Kano `yan uwan juna ne, kuma kan su a hade yake babu wata rarrabuwa.Ya kuma bukaci wadanda suka yi takara tare da su dauki nadin nasa a matsayi nufi ne daga Allah.
Ya ce zai tafiyar da mulkin sa ta hanyar karbar shawarwari daga 'yan majalissar sa da sauran jama`a, kuma zai yi koyi da halayayar marigayi Alhaji Ado Bayero wajen nuna rashin yarda da zalinci.
A game da zangar zangar da ta biyo bayan zaben sa kuwa, mai martaba sarkin na Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi ya tabbatarwa duniya cewa ko kadan masu zanga zangar basu da alaka da masarautar Kano, wasu ne kawai suka fake da wannan dama domin su sukurkutar da kyakkyawan yanayin zaman lafiyar da ake da ita a jihar Kano.
Da yake nasa jawabin, Gwmanan jihar Kano Rabi`u Musa Kwankwaso, ya ce an zabi sabon sarkin ne bisa cancata da kuma shawarwari da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki a kan harkokin masarautar Kano.
Injiniya Rabi`u Musa Kwnakwaso ya tabbatar da cewa ko kadan babu siyasa a batun nadin sabon sarkin. Inda ya ja hankalin al`ummar jihar Kano da kada su amince wasu marasa kishi su yi amfani dasu wajen haifar da rashin kwanciyar hankali a jihar Kano.
Gwamnan ya kuma yi kira ga sabon sarki, da ya yi amfani da basirar sa wajen sake fito da martabar masarautar Kano a duniya baki daya.
Haka zalika ya bukaci sabon sarkin da ya rinka amfani da kyawawan dabarun shugabanci irin na marigayi Alhaji Ado bayero, domin kuwa yin hakan shi ne zai kara tabbatar da kimar masarautar Kano a ko ina.
Daga karshe ya kara kira ga sabon sarkin da ya kasance mai gaskiya da adalci a cikin lamuran sa.
Wamban Kano Alhaji Abbas Sunusi, wanda kuma shine babban dan majalissar sarki ya gabatar da jawabin muba ya`a ga sabon sarkin a madadin sauran `yan majalissar.(Garba Abdullahi Bagwai)