Nadin sabon sarkin ya biyo bayan bukatar da kwamatin zaben sarki na majalissar masarautar Kano ya gabatarwa gwamnatin jihar kamar yadda yake a bisa al'ada.
Kwamitin ya kunshi hakimai hudu ne, wadanda suka kunshi madakin Kano, sarkin Bai, makama da kuma sarkin Dawaki mai Tuta.
Jerin mabukata wannan matsayi da kwamitin ya gabatarwa gwamnan Kano domin amincewa su ne wanban Kano Alhaji Abbas Sunusi da Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero da Lamido Ado Bayero da kuma Malam Sunusi Lamido Sunusi.
Tantance wadannan mutane ya biyo bayan shafe kwanaki biyu ne da 'yan kwamatin suka yi ba tare da barci ba, kafin daga bisani su samu nasarar fitar da wadannan mutane.
Bayan nazartar sunayen jerin mabukatar ne gwamnati ta zabi Malam Sanusi Lamido Sanusi, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya domin ya kasance magajin marigayi Alhaji Ado Bayero.
Malam Sanusi Lamido Sanusi jika ne ga sarkin Kano Muhammadu Sunusi wanda ya mulki Kano daga 1954-1963 yau kusan shekaru 53 ke nan.
An dai samu dan yamutsi a birnin Kano bayan sanarwar da sakataren gwamnatin Kano injiniya Rabi`u Sulaiman Bichi ya gabatar a kafofin yada labarai game da nadin.
Wasu al`umomi dai na ganin gwmanati ba ta yi adalci ba na gaza zabar daya daga cikin 'ya'yan marigayi Ado Bayero ta ba su wannan matsayi.
Ya zuwa yanzu dai al`amura sun lafa bayan baza jami`an tsaro da aka yi a sassan dake cikin birnin Kano. (Garba Abdullahi Bagwai)