Ganawar da shugabannin biyu suka yi jiya Asabar a Abuja, fadar gwamnatin Najeriya, ta zo daidai sa'ar da mayakan kungiyar Boko Haram ke dada kaimi wajen kai hare-hare a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.
Da yake yi wa manema labaru bayani game da ganawar tasu, shugaban kasar Mali Ibrahim Boubakar Keita ya ce ya tattauna da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ne, game da batun tsaro da ya zamewa kasashen nasu babbar matsala, ko da yake dai bai yi wani karin haske game da hakan ba.
Har wa yau batun tabarbarewar tsaro a Mali da Najeriya ne suka mamaye ajandar taron shuwagabannin kungiyar ECOWAS, da aka gudanar a ranar Jumma'a a birnin Accaran kasar Ghana.
Wakilan kungiyar ta ECOWAS sun kuma kalli batun daukar matakan hana yaduwar matsalar ta tsaro zuwa karin wasu kasashen dake yankin yammacin Afirka.
A Najeriya dai hare-haren mayakan kungiyar ta Boko Haram sun haddasa rasuwar sama da mutane 2,000 cikin shekaru biyar, yayin da a Mali kungiyar 'yan kaifin kishin Islama ke ci gaba da dauki ba dadi da dakarun gwamnati a yankuna daban daban dake arewacin kasar. (Saminu)