in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya da Kenya na shirin karfafa shirin bunkasa harkar yawon shakatawa
2014-06-08 16:05:17 cri
Mahukuntan kasashen Najeriya da Kenya sun bayyana shirin su na kaddamar da wani tsari na bunkasa harkar yawon shakatawa a Najeriya, shirin da za a gudanar cikin watanni 12 masu zuwa.

Ministan ma'aikatar al'adu da yawon shakatawar Najeriya Edem Duke ne ya bayyana hakan a birnin Abuja, gabanin bikin kaddamar da fara jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa birnin Nairobin kasar Kenya, wanda kamfanin jiragen saman kasar ta Kenya zai kaddamar.

Mr. Duke wanda ya jaddada muhimmancin harkar yawon shakatawa, ya ce hadin gwiwa da Kenya zai haifar da bunkasar harkokin cinikayya, ya kuma dace da manufar gwamnati mai ci, game da gudanar da sauye-sauye ga kudirorin ci gaban kasar. (Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China