Majiyoyin tsaro da wadanda lamarin ya faru a kan idonsu sun bayyana cewa, an gano gawawwakin maharan guda biyu a wurin da lamarin ya faru, baya ga sama da mutane 15 da suka jikkata wadanda yanzu haka suke karbar magani a asibitin kwararru da ke garin na Maiduguri.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayyana cewa, wannan shi ne hari na farko da mayakan kungiyar Boko Haram suka kaddamar tun lokacin da musulmi suka fara azumin watan Ramadan.
Sai dai kakakin hedkwatar tsaron Najeriya Chris Olukolade ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, mutumin da ake tsare mai suna Babuji Ya'ari wanda shi ma dan kungiyar nan ne ta kato da goro da ke taimakawa jami'an tsaro wajen yaki da 'yan Boko Haram, ana zarginsa da hannu wajen kashe sarkin Gwoza.
Shugaba Jonathan na Najeriya ya bayyana a ranar Litinin kudurin gwamnatinsa na kara yin yaki da ayyukan ta'addanci a kasar. (Ibrahim)