An gudanar da sallar jana`izar ne bayan an kammala sallar Jumma`a da misalin karfe uku na yamma, amma sabo da yawan al`ummar da suka halarci wajen ba a samu damar kai marigayin makabarta ba sai bayan shidda na yamma .
Dukkannin hanyoyin da suka hade da fadar sarkin sun kasance a cunkushe da jama`a da suka fito daga sassa daban daban na duniya.
A wannan lokaci ne sabo da karancin iska da zafin rana wasu suka yi ta suma, lamarin da ya sanya ma`aikatan agaji da sauran jami`an tsaro suka yi ta kokarin aikin ceto, ko da yake dai babu rahoton mutuwa.
Marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya rasu ya bar `ya `ya 62 maza 30 mata 32 a duniya.
Mai shekaru 84, Alhaji Ado Bayero yana daga cikin sarakunan da suka yi kokarin kawo abubuwan ci gaba domin amfanin al`ummar su.
A halin yanzu dai masu nadin sabon sarki suna gudanar da taron sirri domin zabo wanda zai gaji marigayin.
Ana sa ran ranar Lahadin nan ko Litinin 9 ga wata, za a sanar da sabon sarkin. (Garba Abdullahi Bagwai)