140526bagwai.m4a
|
Kamfanin sufurin jiragen saman na Ethopia, wanda ya shafe shekaru masu yawa yana gudanar da harkokin sa a tarayyar Najeriya, inda yake amfani da tasoshin jiragen sama na Legas da Abuja da kuma Fatakwal, yanzu ya fadada zuwa birnin Kano.
A sakamakon wannan cigaba yanzu kamfanin na Ethopian Air ya na amfani da tasoshi hudu ke nan a tarayyar Najeriya .
A lokacin da yake jawabi, yayin wata liyafa da gwamnan Kano Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso ya shiryawa jami`an kamfanin a fadar gwamnati, babban manajan kasuwanci na kamfanin Mr. Ato Busera Awel, yace yanzu kamfanin jiragen na Ethopia yana da jirage 65, wadanda suke zurga zurga a tsakanin kasashe 49 na duniya.
Yace daga cikin wadannan kasashe, a Najeriya da kasar Sin ne kawai kamfanin yake amfani da tasoshin jirage hudu, wajen gudanar da lamuran sa sabo da irin mahimmancin da kasashen ke da su .
A nasa jawabin, jakadan kasar Ethopia a Najeriya Mr. Ali Abdo cewa yayi akwai dadaddiyar dangantaka ta kut da kut tsakanin kasar sa da Najeriya, kuma dukkannin kasashen biyu sun himmatu wajen bunkasuwar harkokin kasuwanci, da kyautatuwar alakar dake tsakanin su.
Yace fadada cibiyoyin sauka da tashin jiragen kasar na Ethoipia zai kara bude kofofin zuba jari a fannoni daban daban na cinikayya.
Da yake nasa jawabin, gwamnan Kano Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso bayyana fara sauka da jirgin na Ehoipia yayi a Kano, a matsayin wata ingantacciyar hanya da zata kara kyautata dangantakar dake tsakanin Najeriya da kasar Ethopia, ya tabbatarwa kamfanin cewa gwamnatin Kano zata yi bakin kokarin ta wajen ba shi duk wani hadin kan daya kamata, domin samun nasarar ayyukan sa.
To sai dai gwamnan ya bukaci kamfanin daya duba yiwuwar daukar yan asalin Kano aiki a bangarori daban daban musamman a ofishin sa dake Kano.
Daga karshe gwamna Rabi`u Musa kwankwaso ya tabbatar da cewa, kafin karewar wa'adin gwamnatin sa zai yi kokarin ganin dukkannin manyan kamfanonin jiragen sama na kasashen waje dake zuwa Najeriya, su na amfani da tashar jirgin sama na kasa da kasa dake birnin Kano.
Gwamnan wanda ya zargin gwamnatin PDP da yin makarkashiya wajen dakile yunkurin wasu kamfanonin jiragen sama sauka a Kano, ya nanata cewa muddin jam`iyyar APC ta samu nasara a zaben 2015, zasu samar da jiragen sama na haya mallakar gwamnati, wadanda za su rika gogayya da na sauran kasashe irin su Ethopia da Masar. (Garba Abdullahi Bagwai)