Wata majiya ta bayyana cewa, a kalla mutane 30 aka kashe a hare-hare daban-daban da mayakan suka kai a kan kauyuka 4 da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno da ke fama da tashin hankali,yayin da a kalla mata da 'yan mata 60 suka bace sakamakon hare-haren mayakan.
Wani malamin addinin Islama mai suna Aminu Mustapha wanda ya gudu zuwa garin Lassa, ya ce tsakanin ranakun Alhamis da Asabar,mazauna kauyukan Gurblagwa,Yafa,Kummabza da Yaza sun shiga wani hali na garari,sakamakon harin da mayakan na Boko Haram suka kaddamar.
Sai dai jami'an tsaro da na jihar ba su yi karin bayani ba game da lamarin.(Ibrahim)