Hukumar bunkasa ci gaban masana'antu ta MDD UNIDO, ta bayyana aniyar tallafawa tarayyar Najeriya wajen aiwatar da tsare-tsare, da za su kai ga cimma nasarar manufofin kasar a fannin bunkasar masana'antu.
Hakan a cewar ministan ma'aikatar lura da masana'antu, cinikayya da zuba jari a kasar Olusegun Aganga, ya biyo bayan kyakkyawan shirin da mahukuntan kasar ke yi a wannan fanni. Inda ya ce hakan ne ma ya sanya gwamnatin kasar mai ci, kaddamar da sabon shirin gaggauta bunkasar masana'antu na NIRP.
Mr. Aganga ya kara da cewa shirin NIRP da za a kwashe shekaru 5 ana gudanarwa, zai share fagen bunkasar kananan masana'antu, da samar da guraben ayyukan yi.
Kaza lika shirin zai bada karfi ga habaka sassan da kasar ke da karfi ta fuskar masana'antu, ciki hadda fannin masana'antu dake sarrafa albarkatun gona, da sashen ma'adanai, da na albarkatun mai da iskar gas da dai sauransu.(Saminu Alhassan)