Yayin ganawar ta su Mr Yatseniuk ya yi fatan dorewar yarjejeniyar da Sin ta cimma da kasar Rasha game da cinikayyar iskar gas ta tsahon shekaru 30.
Sin da Rasha dai sun daddale wannan yarjejeniya ne ran ran 21 ga watan Mayu a birnin Shanghai na nan kasar Sin, yarjejeniyar da ta tanaji cewar Rashan za ta fara samarwa kasar Sin gas daga shekarar 2018, wanda yawan sa zai rika karu a ko wace shekara, ya zuwa cubic mita miliyan dubu 38 cikin shekaru 30 masu zuwa.
Wata jaridar kasar Ukraine ta bayyana cewa, Mr Cai wanda ya halarci bikin rantsuwar sabon shugaban Ukraine Peter Poroshenko, yayi amfani da wannan dama wajen mika sakon fatan alherin shugaba Xi ga sabon shugaban na Ukraine, tare kuma da bayyana muhimmancin da Sin take dorawa, ga dangantaka bisa manyan tsare-tsare, dake tsakanin kasashen biyu.
Ya ce Sin na fatan bunkasa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu bisa ka'idar mutunta juna da mori juna.
A nasa bangare, Peter Poroshenko godiya ya yi ga shugaban Xi, tare da bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na samun bunkasuwa yadda ya kamata, tare da samun ci gaba mai armashi a sassa daban-daban. Poroshenko ya ce yana maraba da ziyarar shugabannin kasar Sin, domin kara karfafa hadin gwiwa, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu. (Amina)