Bugu da kari kuma Mr. Poroshenko ya jaddada cewa, Rasha, babbar kasar dake makwabtaka da kasar Ukraine. Kuma dole sai da taimakon kasar Rasha, wajen kawo karshen yaki da samun zaman lafiya a Ukraine, da ma samun kwanciyar hankali a wannan shiyya.
A waje daya kuma, yankunan da ke kudu maso gabashin kasar Ukraine na ci gaba da cikin halin rudani. A ranar 26 ga wata, sojojin gwamnatin kasar Ukraine sun tafka karamin fada da dakaru a filin jiragen sama na birnin Donetsk, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum a kalla daya. Kuma bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Rasha ya bayar, an ce, sojojin kasar Ukraine su yi amfani da jiragen sama masu saukar ungulu 6 zuwa 8, da kuma jiragen saman yaki 2 wajen luguden boma bomai, a yayin dakarun 'yan a ware suka rika amfani da makaman roka domin maida martani. (Kande Gao)