in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihohin biyu dake gabashin Ukraine sun sanar da ballewarsu daga kasar
2014-05-13 14:30:37 cri
A ran 12 ga wata, jihohin Donetsk da Luhansk Oblast dake gabashin kasar Ukraine sun sanar da ballewarsu daga kasar, bayan fitar sakamakon kuri'ar raba gardamar da suka kada a ranar Lahadin da ta gabata. Hakan dai ya shaida aniyar su ta kasancewa kasashe masu cin gashin kansu.

Game da hakan a yayin wani taron ministocin kungiyar tarayyar kasashen Turai da aka yi a jiya Litinin, babbar wakiliya kan manufofin diflomasiyya da tsaron kungiyar EU Catherine Ashton, ta bayyana cewa rashin daukar matakan da suka wajaba da kasar Rasha ta yi ne ya hana samar da damar warware rikicin kasar Ukraine yadda ya kamata. Lamarin da kuma ya haddasa tabarbarewar yanayin kasar ta Ukraine, wanda kuma ya sanya ministocin kungiyar cimma matsayar kara kakaba wa kasar ta Rasha takunkumi.

Shi kuwa shugaban majalisar dokokin kasar Ukraine wanda a halin yanzu ke rikon kwaryar shugabancin kasar Oleksander Turchynov cewa ya yi, bai amince da kuri'ar raba gardamar da aka yi a wadannan jihohi ba, kuma za a hukunta wadanda suka shirya hakan. Bugu da kari, Turchynov ya kara da cewa, yana fatan yin shawarwari tare da wadanda ke son a kawo karshen riciki da kuma gabatar da bukatunsu bisa doka.

Kaza lika ita ma hukumar yada labarai ta fadar gwamnatin kasar Rasha ta bayyana cewa, Rashan na mai da hankali kan kuri'ar raba gardama da aka gudanar a wandannan jihohi biyu, tare da girmama kudurin da jama'ar jihohin suka yi cimma ga kawunansu.

Bugu da kari shugaban kwamitin kula da harkokin Turai Herman Van Rompuy ya bayyana a birnin Kiev cewa, kungiyar EU tana goyon bayan cikakken ikon yankunan kasar Ukraine, da kuma 'yancin kanta, ba kuma ta amince da sakamakon kuri'ar raba gardamar da jahohin biyu suka gudanar ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China