A cikin sanarwar da ta gabatar, madam Jen Psaki ta bayyana cewa, bisa ga abubuwan dokokin Ukraine suka tanada, an ce, zaben raba gardamar da dakarun dake neman kawo wa kasar baraka suka shirya a jihohin biyu dake gabashin kasar haramtaccen aiki ne, kuma ya saba wa dokokin kasa da kasa da kawo illa ga kiyaye cikakken yankin Ukraine. Haka zakila, kasar Amurka ta nuna wa kasar Rasha bacin ranta game da gazawar da ta nuna wajen hana wannan zaben raba gardama. Tare kuma da nuna dari dari kan aikin janye jiki da sojojin kasar Rasha suka yi daga kan iyaka da kasar Ukraine.
Bisa sakamakon zaben da kwamitin zabe mai zaman kansa na Jamhuriyar Jama'ar Donetsk ya gabatar a daren ranar 11 ga wata, ya nuna cewa zaben raba gardama da aka yi kan batun neman samun 'yancin jihar Donetsk, ya samu amincewa da kashi 89.07 cikin dari.(Kande Gao)