A yayin taron, shugaban rikon kwarya na kasar kuma shugaban majalisar dokokin kasar Oleksander Turchynov ya bayyana cewa, gwamanti za ta dauki matakai bisa tsarin mulkin kasar, da kuma dokokin kasar kan wadanda abin ya shafa, da nufin hukunta dakaru masu neman aiwatar da hare-hare a kasar, da kuma wadanda ke tursasa bukatun kasashen ketare kan jama'ar kasar.
Bugu da kari firaministan kasar Ukraine Arseniy Yatsenyuk ya bayyana a yayin taron cewa, ya kamata a samu daidaito kan karin yarjejeniyar neman warware matsalar Ukraine bisa tsarin Geneva, wanda kasar ta samun halarta. Shawarwarin da kuma Ukraine din, da Kungiyar EU, Amurka da kuma Rasha suka aiwatar a tsakaninsu.
Aikin mafi muhimmanci dake gaban gwamnatin kasar Ukraine a halin yanzu shi ne, na tabbatar da tsaron al'ummomin kasar, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
Dangane da wannan lamari, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana a wannan rana cewa, sakamakon tashe-tashen hankulan da ke ci gaba da faruwa a kasar ta Ukraine, babban zaben da za a yi a kasar Ukraine ba zai samu halarci ba.
A wata sabuwa kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev ya furta a ran 14 ga wata cewa, kasar Rasha ba za ta koma teburin shawarwari tare da kasar Ukraine kan farashin iskar gas ba, har sai kasar Ukraine ta biya ta wasu basussuka na iskar gas din da take bi ta. (Maryam)