in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Rasha sun jawo hankula yayin bikin taya murnar ranar cika shekaru 70 da kama Normandy
2014-06-06 11:06:10 cri

A jiya Alhamis ne shugaban kasar Faransa François Hollande ya karbi bakuncin shugabannin kasashe da dama, yayin da ake jajiberin cika shekaru 70 da kama Normandy.

Taron dai ya ba shi damar haduwa da shugaba Barack Obama na Amurka da takwaransa na Rasha Vladimir Putin daya bayan daya, lamarin da ya jawo hankulan masharhanta.

Yayin taron shugabannin, Hollande ya gana da shugaba Obama, kafin daga bisani ya zanta da Vladimir Putin, a matsayin su na masu wakiltar ra'ayoyi biyu mabanbanta game da batun kasar Ukraine.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Holland ya gana ne da Obama yayin liyafar cin abincin dare, inda suka yi musanyar ra'ayoyi kan halin da ake ciki a Ukraine, da batun makaman da Faransa ta sayarwa Rasha, da matakin da Amurka ta dauka kan bankin Paris da dai sauransu.

Jim kadan da ganawar tasu, Hollande ya gana da shugaba Putin a fadar sa dake Elysée. An ce yayin tattaunawar da suka yi shugaba Hollande ya yi kokarin sulhunta Amurka da Rasha, game da takaddamar su kan Ukraine.

Kuma ko da yake shugabannin Amurka da Rasha ba su gana da juna kai tsaye ba, a hannu guda ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov, da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry sun gudanar da shawarwari. Inda bayan ganawar tasu, Lavrov ya bayyana cewa, kamata ya yi Amurka ta ja hankalin gwamnatin Ukraine, wajen ganin ta dauki matakai da za su kawo karshen tashe-tashen hankula da nuna karfin tuwo. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China