A ranar Talata 20 ga wata, majalisar dokokin kasar Ukraine ta zartas da "Takardar bayani kan hakuri da juna da zaman lafiya" ta hanyar kada kuri'a.
A cikin takardar, an bayyana cewa, majalisar ta goyi bayan "Takardar Geneva" da Ukraine da Amurka da kungiyar EU da kuma Rasha suka cimma matsaya a kai a ranar 17 ga watan jiya, haka kuma ta nuna goyon baya da a tattauna a duk fadin kasar bisa tsarin taron sulhuntar al'umma, da shirya babban zabe a ranar 25 ga wata.
Bugu da kari kuma majalisar ta yi Allah wadai da yin amfani da makamai ba bisa doka ba da kuma ta da hargitsin nuna kin jinin juna.(Kande Gao)