A yayin taron manema labaran da aka yi a wannan rana, Mr. Lukashevich ya bayyana cewa, kasarsa ta damu matuka kan yadda al'amura ke tabarbarewa a kasar ta Ukraine, kuma gwamantin kasar Ukraine na ci gaba da keta hakkin jama'arta.
A wannan rana kuma, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta ba da wata sanarwar, inda ta nuna cewa, ya kamata a fara gudanar da taron sulhunta al'ummar Ukraine, a kokarin da ake na yin kwaskwarima ga tsarin mulkin kasar, ta yadda za a iya tabbatar da shigar da dukkan bangarorin siyasa dake sassa daban daban na kasar cikin wannan yunkuri.
A nata bangare kuma, ma'aikatar harkokin wajen kasar Ukraine ta ba da wata sanarwa, inda ta nuna rashin jin dadinta kan atisayen soja da kasar Rasha ta yi a kan iyakar kasashen biyu, inda ta bukaci kasar Rasha da ta janye sojojinta daga wannan yanki. (Maryam)