A hannu guda kuma, kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, Ban Ki-moon yana fatan Poroshenko zai dauki matakai cikin sauri, na kawo karshen rikicin siyasa, da na tattalin arzikin kasar. Baya ga batun inganta zamantakewar al'umma, da kuma habaka tsarin dimokuradiyya a kasar.
Mr Ban ya bayyana farin cikin sa game da alkawarin da Poroshenko ya yi, na sassauta halin da kasar ke ciki, da fara yin shawarwari a cikin kasar, da kuma tsakanin kasar da sauran kasashe makwabtaka da ita.
Bugu da kari bisa bukatar wakilin kasar Ukraine, kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da wani taro kan halin da Ukraine din ke ciki, inda mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min, ya bayyana cewa, kasar Sin na girmama zaben da jama'ar kasar Ukraine suka yi.
Ya kara da cewa, kawo yanzu dai ana ci gaba da samun rikice-rikice a kasar ta Ukraine, wadanda suka haddasa mutuwa, da raunatar jama'a da dama, da kuma hasarar dukiya mai tarin yawa. Kasar Sin dai na kulawa da halin da ake ciki, tana kuma fatan bangarori daban daban da abin ya shafa, za su yi shawarwari, su kuma warware rikicin kasar ta hanyar siyasa, matakin da Sin din ta yi alkawarin marawa baya. (Zainab)