Hukumar zaben kasar Ukraine ta sanar da cewa, bisa sakamakon kidayar kuri'un da daukacin mambobin hukumar su 15 suka sanyawa hannu, yawan kuri'un da Poroshenko ya samu ya kai kashi 54.7 cikin dari, yayin da tsohuwar firaministar kasar Yulia Tymoshenko ta kasance ta biyu cikin 'yan takara 21 da suka fafata a neman kujerar shugabancin kasar ta Ukraine.
Kakakin magatakardar MDD Ban Ki-moon, Stephane Dujarric ya bayyana cewa, Ban Ki-moon ya zanta da zababben shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ta wayar tarho a makon da ya gabata, inda ya shawarce shi da ya yi amfani da hanyar lumana wajen gudanar da aikin sa.
Dujarric ya ce, yayin waccan tattaunawa Mr. Ban ya bayyana cewa, ya fahimci bukatun gwamnatin kasar Ukraine na kiyaye ikon yankunan ta, don haka kamata ya yi a yi amfani da hanyoyi na lumana wajen kaiwa ga nasara. Har ila yau babban magatakardan MDD ya yi kira ga Poroshenko da ya yi shawarwari da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Ana dai sa ran gudanar da bikin rantsuwar kama aikin sabon shugaban kasar ta Ukraine a ranar 7 ga watan nan na Yuni. (Zainab)