in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Poroshenko ya ci zaben shugaban kasar Ukraine
2014-05-30 15:23:06 cri
Hukumar zaben kasar Ukraine ta gabatar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar a ranar 29 ga wata, inda ta sanar da cewa, Petro Poroshenko ya samu kuri'u kashi 54.7 cikin kashi dari, rinjayen da ya ba shi damar zama sabon shugaban kasar. Kotun tsarin mulkin kasar Ukraine ta tsaida kudurin cewa, wa'adin shugaban kasar a wannan karo shi ne shekaru 5.

Tsofuwar firaministar kasar Ukraine, Yulia Tymoshenko ta samu kuri'u kashi 12.81 cikin kashi dari, wanda ya bata damar kasance ta biyu a cikin 'yan takara 21 da suka neman kujerar shugabancin kasar Ukraine a wannan karo.

Kasashen Amurka, Rasha da kungiyar EU da sauran kasashe da hukumomin duniya sun bayar da sanarwa, inda suka bayyana fatansu na yin shawarwari da hadin gwiwa a tsakaninsu da sabon shugaban kasar Ukraine. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China