A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya yi taron gaggawa kan halin da ake ciki a Ukraine. A cikin jawabinsa, Liu Jieyi ya bayyana cewa, a kwanan baya, yanayin da ake ciki a wasu yankunan dake kudu maso gabashin Ukraine ya tsananta, inda lamarin yayi sanadiyyar mutuwar mutane da jikkatar wasu. Sin tana mai da hankali kwarai kan wannan batu. Sau da yawa ne Sin ta bayyana matsayinta kan batun Ukraine. Kuma tana fatan bangarorin daban daban za su yi la'akari da moriyar al'ummomin Ukraine, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya domin kauracewa kara tsanantar rikici.
Dadin dadawa, Liu Jieyi ya kara da cewa, hanyar daidaita batun Ukraine a siyasance, it a ce hanya daya tak da za a bi. Idan ana fatan daidaita rikicin Ukraine yadda ya kamata, dole ne a yi la'akari da tarihi da hakikanin yanayin da ake ciki a yanzu, da mai da hankali kan iko da moriya da bukatun al'ummomi dake yankuna daban daban na kasar, a kokarin samun daidaito bisa la'akari da moriyar kowa ne bangare.(Fatima)