Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi tir da babbar murya, da a saki ma'aikatan kungiyar tsaro da hadin kai ta Turai, wadanda aka tsare a gabashin kasar Ukraine.
Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar a jiya Litinin, Mr. Ban ya bukaci dakarun da suka kame jami'an da su gaggauta sakin su ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Har wa yau a dai wannan rana, shi ma wakilin Rasha da ke kungiyar tsaro da hadin kai ta Turai Andrei Kelin, ya ce, game da burin da ake da shi na sakin ma'aikatan, Rasha ta riga ta gudanar da wasu shirye-shirye na hakika, ba kuma batu ne Rashan ke yi na fatar baki ba kadai.
A makon jiya ne dai wasu dakarun da ke adawa da gwamnati a gabashin Ukraine, suka kame wata tawagar hadin gwiwa ta kungiyar tsaro da hadin kai ta Turai, mai kunshe da ma'aikata 8 da wasu jami'an sojan Ukraine. Tuni dai kungiyar tsaro da hadin kai ta Turai ta riga ta tura wata tawagar tattaunawa da nufin kawo karshen al'amarin, sai dai kawo yanzu dakarun ba su saki mutanen ba, in ban da wani guda sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita. (Danladi)