Da misalin karfe 8 na daren jiya Lahadi ne aka kamala kada kuri'ar babban zaben shugaban kasar Ukraine, inda binciken jin ra'ayoyin jama'a ya nuna cewa, 'dan takara Petro Poroshenko ya samu kuri'u fiye da kashi 50 bisa dari, wanda ake zaton zai ci nasara a yayin babban zaben.
Babbar hukumar bin bahasi ta kasar Ukraine ta bayar da wata sanarwa bayan kada kuri'un, inda ta ce, ban da jihohin Donetsk da Luhansk da ke gabashin kasar, wadanda suka sanar da samun 'yancin kansu, sauran jihohin kasar sun gudanar da zaben yadda ya kamata. A wadannan jihohi biyu, dakarun kungiyoyin jama'a sun kawo cikas ga zaben, sakamakon haka ba a gudanar da zabe yadda ya kamata ba a wasu wuraren.
A ranar zaben, shugaban Jamhuriyar jama'ar kasar Donetsk Denis Pushilin ya sanar da cewa, kasarsa da Jamhuriyar jama'ar kasar Luhansk sun daddale hadaddiyar sanarwa ta kafa kawance, inda za su kafa majalisar dokoki ta kawancensu. Sai dai wani shugaba a Jamhuriyar jama'ar kasar Donetsk Pavel Gubarev ya ce, ba za su amince da sabon shugaba da zababiyar majalisar Ukraine za ta bayyana ba, sabo da tuni Donetsk da Luhansk suka zamo kasashe biyu masu zaman kansu.
A wani ci gaban kuma, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa, Amurka tana sa ran hadin kai da sabon shugaba da sabuwar majalisar Ukraine za ta zaba, don nuna goyon baya ga gyare-gyare a fannonin siyasa da tattalin arziki a kasar. (Danladi)