Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya bayyana a ran 19 ga wata cewa, Rasha ta sake yin kira ga mahukuntan Kiev da su daina daukar matakan soja da sunan yaki da ta'addanci. A sa'i daya kuma, babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Ande rs Fogh Rasmussen yana sa ran alheri ga shawarwarin da za'a yi da Rasha a makon gobe kan halin da ake ciki a Ukraine.
Wata sanarwar da muka samu daga ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta nuna cewa, bayan da Lavrov ya yi shawarwari da ministan kula da harkokin diplomasiyya da harkokin Turai na kasar Slovak Miroslav Lajcak a ran 19 ga wata, ya ce, wani sharadin da ya wajaba domin gudanar da shawarwari a duk fadin kasar Ukraine shi ne, a daina daukar matakan soja da sunan yaki da ta'addanci a kudu maso gabashin kasar. Rasha ta sake yin kira ga mahukuntan Kiev da su aiwatar da yarjejeniyar Geneva da shirin tasiwirar kungiyar tsaro da zaman lafiya ta Turai, tare da daina daukar matakan soja da sunan yaki da ta'addanci.
Babban sakataren kungiyar NATO Rasmussen ya bayyana a ran 19 ga wata cewa, NATO ta gabatar da bukatar kira taron manyan jami'ai a tsakaninta da Rasha. NATO tana fatan za a kira taron a makon gobe, amma Rasha har yanzu ba ta mayar da martani ba. Rasmussen ya yi nuni da cewa, ko da yake NATO za ta dakatar da hadin kai da Rasha, amma kwamitin kula da harkokin NATO da Rasha zai ci gaba da aiki ta yadda bangarorin biyu za su iyar cudanya yadda ya kamata a kan batutuwan Ukraine. (Danladi)