Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika gaisuwa ga rundunar sojan da aka girke a jihar Xinjiang, yayin da ya kai musu ziyara daga ran 27 zuwa 29 ga watan Afrilu da ya gabata, inda kuma ya nazarci yadda za a gudanar da aikin kiyaye zaman karko da kare rayuka da dukiyoyin jama'a. Ban da haka kuma a madadin kwamitin tsakiyar na jam'iyyar Kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwa da rundunar sojan kasar, ya mikawa daukacin jami'an soja da wadanda suka shirya shiga soja gaisuwa. Inda Mr Xi ya jaddada cewa, ya kamata a cimma burin JKS na karfafa sojojin kasar, ta yadda za a kare martabar su a dukkan fannoni domin ba da tabbaci ga zaman karko da kwanciyar hankali cikin dogon lokaci a jihar Xinjiang. (Amina)