Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya komo gida Beijing yau Laraba bayan da ya kammala ziyarar aiki zuwa kasashen hudu dake Turai.
Wannan ziyarar aikin, wacce ya fara tun daga 22 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Afrilu ta kai shi kasashen Netherlands, Faransa, Jamus da Belgium.
A yayin wannan ziyara, shugaban kasar ta Sin, ya halarci taron koli na uku a kan nukiliya wanda aka yi a Hague na kasar Netherlands.
Hakazalika a lokacin wannan ziyara, shugaba Xi, ya kuma ziyarci babbar hedkwatar hukumar ilmi, da fasaha da al'adu ta majalisar dinkin duniya dake birnin Paris na Faransa, da kuma hedkwatar kungiyar tarayyar Turai dake Brussels. (Suwaiba)