Bayan shawarwarin da ya yi tare da shugaban kasar Sin Xi Jinping, Mr. Schultz ya bayyana ta gidan talebijin na kungiyar EU cewa, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, na da muhimmiyar ma'anar tabbatar da zaman karko, da raya tattalin arzikin kasa da kasa. Ya kuma kara da cewa, za a iya kyautata dangantakar bangarorin biyu bisa fannoni daban daban a nan gaba. Ya ce, kamata ya yi bangarorin biyu su dukufa cikin hadin gwiwa, domin samar da dauwamammen ci gaban tattalin arziki, da kuma karin guraben aikin yi cikin shekaru masu zuwa.
Bugu da kari, Mr. Schultz ya ce, bai kamata a takaita hadin gwiwar bangarorin biyu a fannin ciniki ba kawai, ya ce, kamata ya yi a karfafa shawarwarin siyasa dake tsakanin kasar ta Sin da kasashen Turai, ta yadda za a iya samun karin sakamako mai gamsarwa a dangantakar bangarorin biyu. (Maryam)