in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya bayar da wani jawabi mai muhimmanci a Cibiyar nazarin harkokin Turai
2014-04-02 09:07:38 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin jawabi, a cibiyar nazarin harkokin Turai da ke birnin Brussels na kasar Belgium, inda ya karfafa cewa, bin tarin gargajiya a fannonin al'adu, da tarihi, da halin kasar na musamman, na tabbatar da cewa, dole ne kasar Sin ta ci gaba da bin hanyar musamman da ta dace da halinta.

Bugu da kari, shugaba Xi ya ce bisa burin ciyar da dangantakar Sin da Turai gaba, kamata ya yi bangarorin biyu su zurfafa fahimtar juna, da kokari tare, wajen kafa ginshikan wanzar da zaman lafiya, da bunkasuwa, da yin gyare-gyare, da raya al'adu a tsakaninsu.

Shugaba Xi ya kara da cewa, yana gudanar da wannan ziyara ne, da fatan kafa wata gadar aminci da hadin kai, a tsakanin nahiyoyin Asiya da Turai, bisa kokari tare da kawayen nahiyar na Turai, domin ciyar da dangantakar dake tsakani gaba. Ya ce Sin na fatan kara fahimtar Turai, a yayin da nahiyar Turai ke bukatar kara fahimtar kasar Sin.

Xi ya karfafa cewa, muddin aka jingine tarihin kasar Sin, da al'adun ta, da tunanin Sinawa, da sauyin zamanin da kasar ke fuskanta, ba za a iya fahimci hakikanin kasar Sin ba.

Bugu da kari, kasar Sin ba za ta iya kwaikwayon dukkan tsarin siyasa, da hanyoyin bunkasuwa, ba tare da yin gyare-gyare ba, muddin dai tana fatan amfana daga hanyoyin yadda ya kamata, tare da kokarin kaucewa kalubale dake tattare da hakan.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, Sin da Turai suna cikin wani muhimmin lokaci na samun bunkasuwa, suna kuma fuskantar dama da kalubale da ba a taba ganin irinsu a baya ba. Ya ce ya dace sassan biyu su yi kokari tare, wajen kafa gadojin nan Hudu, na bunkasa zaman lafiya, da aiwatar da gyare-gyare, da inganta al'adu a tsakaninsu, ta yadda za su iya raya dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, irin dangantakar dake da tasiri babba ga duniya baki daya. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China