Shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya gana da sarkin kasar Belgium Philippe Leopold Louis Marie a ran 30 ga watan Maris a birnin Brussels.
Xi ya ce, dangantakar da ke tsakanin Sin da Belgium tana samun cigaba sosai, kuma kasar Sin ta nuna yabo ga wannan cigaba. Ya kara da cewa, Belgium ta kasance hedkwatar kungiyar tarayyar Turai wato EU, sabo da haka ne kasar ta zama wata zuciyar Turai, bugu da kari kuma tana kasancewa wata muhimmiyar abokiyar kasar Sin wajen hadin gwiwa. Xi ya bayyana fatan cewa ziyararsa, za a kara ciyar da dangantakar Sin da Belgium da kuma Sin da Turai gaba.
A nasa bangare Sarki Philippe ya yi nuni da cewa, shugaba Xi shi ne shugaba na farko da ya karbi bakunci tun bayan da ya kama aikinsa, da ya kawo ziyarar aiki a kasar, don haka wannan babbar alfarma ce ga kasar Belgium. Sarakunan Belgium da gwamnatinta za su ci gaba da aiwatar da manufofin abokantaka tare da kasar Sin kamar yadda aka saba yi tun fil azal, suna son kara ba da taimakon musamman ga bunkasuwar dangantakar Turai da Sin.
A ganawarsu, sarki Philippe ya ba da kyautar Leopold da takardar yabo ga shugaba Xi. Kyautar Lepold ta kasance lambar yabo mafi girma ta kasar Belgium, wadda sarki ya kan bada wa da kansa, ga wadanda suka ba da muhimmin taimako ga kasar.
Haka kuma, a cikin hadin gwiwa ne, shugaba Xi da sarki Philippe suka halarci bikin bude lambun Panda na gidan ajiye dabbobi mai suna 'Pairi Daiza'. (Danladi)