Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Brussels na kasar Belguim a yau Lahadin nan, domin fara ziyarar aiki, tare kuma da kai ziyara hedkwatar kungiyar kawancen kasashen Turai.
Da misalign karfe 9 da minti 15 na safiya ne dai jirgin saman musamman na shugaba Xi ya sauka filin jirage na Abelag, inda firaministan kasar Belgium Elio Di Rupo ya tarbe shi, tare da uwargidan sa Peng Liyuan.
Mr Xi ya bayyana cewa, yana fata wannan ziyara zata bada damar zurfafa mu'ammala tsakanin kasashen biyu, ta yadda za su kara fahimtar juna, da zurfafa dankon zumunci, da bunkasa dangantakar dake tsakanin su zuwa sabon mataki.
A hanlin yanzu, Sin da Turai na wani muhimmin lokaci na samun bunkasuwa, inda sassan Biyu ke samun sabon zarafi na ci gaba. Matakin da ya sanya shugaban na Sin bayyana fatan bangarorin biyu, za su kara yin musayar ra'ayi, kan zurfafa hadin gwiwa, da bunkasa moriyar juna, da habaka dangantar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, ta yadda za a ciyar da dangantakar dake tsakaninsu gaba. (Amina)