in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba za ta canja manufar inganta hadin kai da kasashen Afirka ba, in ji shugaba Xi Jinping na kasar Sin
2014-04-08 16:09:11 cri

Shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya bayyana a ran 8 ga wata a nan birnin Beijing cewa, inganta hadin kai da kasashen Afirka, ya zama wani muhimmin tushe na manufofin diplomasiyya na kasar Sin, wanda kasar Sin ba za ta canza shi sakamakon bunkasuwarta da kyautatuwar matsayinta a duniya ba.

Yayin da yake ganawa da firaministan Namibiya Hage Geingob a ranar, shugaba Xi ya yi nuni cewa, wajen hada kai da kasashen Afirka, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan ra'ayin daidaici da samun moriyar juna, tana mai da hankali kan karfafa kwarewarsu wajen samun bunkasuwa, da samar wa jama'ar kasashen Afrika moriya ta yadda za'a cimma burin samun moriya da nasarori tare. Xi ya kara da cewa, ya kamata Sin da Namibiya su kara yin cudanya da shawarwarin siyasa, da nuna goyon baya ga juna a kan manyan batutuwa. Kasar Sin tana ba da kwarin gwiwa ga kamfanonin kasar da ke da kwarewa da amana da su je Namibiya, don su hada kai da kasar a fannonin ma'addinai, noma, ayyukan more rayuwar jama'a, kirkire-kirkire da manyan ayyuka.

A ganawarsu, mista Geingob ya ce, Namibiya tana son zurfafa dangantakar abokantaka da hadin kai tare da Sin, tana son bullo da wani yanayi mai kyau ga kamfanonin Sin domin zuba jari a kasarsa. Namibiya tana son kara ba da taimako ga ci gaban huldar da ke tsakanin Afirka da Sin.

Bayan haka kuma, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Mista Yu Zhengsheng shi ma ya gana da firaministan Namibiya Mista Hage Geingob. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China