Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi kira da a dauki karin matakan bunkasa dangantakar dake tsakanin kasarsa, da kungiyar tarayyar Turai ta EU, matakin da zai ba da dama ga sassan biyu su amfana da juna daga dukkanin fannoni.
Shugaba Xi, wanda ya bayyana hakan yayin ganawarsa da shugaban hukumar Turai Manuel Barroso, ya ce, duba da halin da ake ciki na dunkulewar tattalin arzikin duniya, Sin da tarayyar Turai na da bukatu masu alaka da juna, don haka ya dace su dukufa, wajen daukar matakan da za su ba su damar kara cin moriyar juna, da karfafa dangantakar dake tsakanin su.
Bugu da kari, Xi ya ce, kamata ya yi Sin da kungiyar ta EU, su martaba tsarin ci gaba, da na zamantakewar juna, tare da karfafa tsarin tattaunawa, da musayar tsare-tsaren kawo sauyi domin ci gaba tare. Kaza lika, shugaban na Sin ya ce, ya dace sassan biyu su ci gaba da girmama juna, tare da kauda banbance-banbancen dake tsakanin su, domin cimma bukatar da suka sanya gaba.
A nasa bangare, Mr. Barroso ya yaba da irin ci gaban da dangantakar Sin da tarayyar Turai ke samu, yana mai cewa, EU na yabawa da goyon bayan da Sin ke baiwa kasashe mambobin ta a lokacin da suke fuskantar kalubale daban daban.
Ya ce, EU na mai da hankali kwarai, ga ci gaban da Sin ke samu, da ma batun sauye-sauye da take gudanarwa. Za kuma ta baiwa kasar goyon bayan da ya dace, domin cimma nasarar bunkasa dangantakar dake tsakanin su. (Saminu)