Yayin ganawarsa da Shugabar birnin Hannelore Kraft, shugaba Xi bayyana cewa, jihar na daya daga cikin jihohi masu karfin tattalin arziki, da ke da dinbin al'umma Jamusawa, wanda hakan ya sanya ta kasancewa mai matukar muhimmanci a fannin cinikayya, da zuba jari, da hadin gwiwa tsakanin Sin da Jamus.
Ya ce jihar ta samu babban ci gaba a fannonin sauya hanyar bunkasar tattalin arziki, da samun dauwamammen ci gaba, a sabili da haka, bangarorin biyu na iya zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu. Xi ya kara da cewa, Sin na maraba da jihar North Rhine-Westphalia, a fagen shirin bunkasa tattalin arziki na hanyar siliki, musamman ta hanyar amfani da matsayin musamman na tashar jirgin ruwan Duisburg. Har wa yau Sin ta yi imanin cewa, za a samu karin sakamako mai ma'ana a wajen hadin gwiwa tsakanin Sin da wannan jiha.
A nata bangare, Kraft cewa ta yi, jihar North Rhine-Westphalia, za ta yi hadin gwiwa da Sin yadda ya kamata. Ta ce yanzu haka akwai kamfanonin Sin sama da 800 a jihar, yayin da kamfanonin jihar sama da 1000 suka zuba jari a kasar Sin. Kazalika Jihar na fatan karfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakaninta da Sin a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da sufuri, baya ga jigilar kayayyaki, da musayar al'adu da dai sauransu. Duka dai a kokarin kara taka rawar gani a fannin bunkasa dangantaka tsakanin Jamus da Sin.
Dadin dadawa, shugaba Xi ya gana da mataimakin firaministan kasar, kuma minista mai lura da harkokin tattalin arziki da makamashin kasar ta Jamus Sigmar Gabriel a birnin na Dusseldorf.(Fatima)