in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin na daya daga cikin fitattun mutane dari da suka fi kawo taimako ga duniya
2014-04-25 15:57:28 cri

Mujallar Time ta kasar Amurka ta gabatar da sunayen mutane dari da suka fi ba da gudunmawa a duniya a shekarar 2014, bisa shafin yanar gizonta a ran 24 ga wata. Shugaban kasar Sin Xi Jinping na daga cikin fitattun mutanen wannan zabe. Haka kuma an zabi shugaban kasar Amurka Barack Obama, da shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin.

Tsohon jakadan Amurka a kasar Sin, John Huntsman wanda ya rubuta shahin wannan mujalla ya ba da bayani kan mista Xi cewa, shi ya kasance wani babban shugaban dake yin kwaskwarima mai zurfi a kasar Sin tun bayan tsohon shugaban kasar, marigayi Deng Xiaoping, kuma tunaninsa, mutuncinsa da ma hallayarsa suna cigaba da jawo hankalin shugabannin duniya sosai. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China