Shugaban kasar ta Sin wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar, yayin ziyarar sa a tashar ruwan Duisburg, ya ce aiwatar da wannan shawara, mataki ne da zai bunkasa tattalin arzikin sassan Biyu ta fuskar cinikayya bisa sabon salo, kamar yadda a baya hanyar Siliki ta haifarwa sassan Biyu damar kulla nagartaccen tsarin kasuwanci mai cike da riba.
Shugaba Xi ya ce Kasashen Sin da Jamus, manyan bangarori ne Biyu, mafiya girma a tsagin nahiyoyin Asiya da Turai, wadanda ke da ikon daga matsayin hada-hadar cinikayya, da kasuwanci tsakanin nahiyoyin Biyu zuwa matsayi na gaba.
Don haka ne ma ya bayyana shawarar hadin kan kasashen Biyu, wajen gina wannan sabon tsarin bunkasa tattalin arziki da cinikayya ta hanyar kafa yankin Siliki, kari bisa layin dogo na Chongqing-Xinjiang da ta hade Sin da sassan nahiyar Turai. (Saminu Alhassan)