Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya samu wannan labari, nan da nan ya ba da umurnin daukar matakin da ya dace wanda za a kwashe dogon lokaci domin gudanar da shi, haka kuma ya kamata a ba shi muhimmanci sosai. A cewar shugaban kamata ya yi, jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta ba da kulawa da wadanda suka raunana cikin lokaci da bincike kan al'amari ta yadda za a yanke hukunci ga wadanda suka aikata laifin yadda ya kamata. Kamata ya yi, a kwantar da hankulan jama'a da ba da tabbaci ga kare lafiyar jama'a da dukiyoyinsu. (Amina)