in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da shugabannin nahiyar Turai
2014-03-31 20:49:07 cri
Shugaban kasar Sin Mr Xi Jinping ya gana da shugaban kwamitin gudanarwa na nahiyar Turai Herman Von Rompuy a ran litinin din nan 31 ga wata a birnin Brussels,inda shugabannin biyu sun yi musanyar ra'ayi kan yadda za su zurfafa dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni bisa ga sabon halin da ake ciki, tare da cimma matsaya daya.

A jawabin sa Mr Xi ya jaddada cewa, ya kamata a dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, da kuma hada karfinsu, kasuwaninsu da al'adunsu tare ta yadda za a bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Turai a fannoni hudu.

Na farko in ji shi shi ne zaman lafiya, sai samun bunkasuwa, da yin kwaskwarima da al'adu, ta wadannan fannoni ne za a yi kokarin ciyar da hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2 gaba, gami da ba da gudunmawa wajen bunkasa kasashen duniya.

Ban da haka, Mr Xi ya nuna cewa, Sin da Turai na dogaro da juna sosai bayan bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu a cikin shekaru 40 da suka gabata. Ba ma kawai, dangantakar dake tsakaninsu na da alaka da bunkasuwarsu, har ma zai kawo amfani ga tsarin duniya a fannin siyasa da tattalin arziki.

Shugaba Xi don haka ya ce a nata bangare, kasar Sin na mai da muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da nahiyar Turai, kuma tana goyon bayan kasashen Turai a kokarinsu na samun tsarin bai daya, saboda da haka Sin na fatan kara zurfafa dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu nan gaba.

Ban da haka kuma,Shugaban kasar na Sin ya gana da shugaban majalisar dokokin Turai Mr Martin Schulz da shugaban kwamitin kungiyar kawancen kasashen Turai EU Jose Barroso duk a birnin Brussels na kasar Belgium a litinin din nan 31 ga wata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China