Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi shawarwari tare da shugabar gwamnatin kasar Jamus, Angela Merkel a jiya 28 ga wata a birnin Berlin na kasar Jamus, inda suka yi musayar ra'ayoyi sosai kan dangantakar dake tsakanin kasashensu, da kuma maida hankali kan manyan batutuwan da suka shafi harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, dake janyo hankulansu, tare da cimma muhimmin ra'ayi daya kansu. Har illa yau sun tsaida kudurin ingiza huldar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayin dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, ta yadda za'a tabbatar da burin da za a cimma wajen bunkasa makomar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Bayan shawarwarin kuma bangarorin biyu sun bayar da hadaddiyar sanarwa game da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin kasashen Sin da Jamus.
Haka zalika shugabannin biyu sun halarci bikin sanya hannu kan takardun hadin kai tsakanin kasashen biyu, da suka shafi fannonin motoci, sufuri, sadarwa, haraji, kudi, da dai sauransu. (Bilkisu)