in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya tsawaita lokacin aikin kafa zaman lafiya a CAR na shekara daya
2013-01-25 11:16:29 cri
A ranar Alhamis ne, kwamitin sulhu na MDD ya yanke wani kuduri na bai daya, don karawa ofishin aikin kiyaye zaman lafiya da ake kira BINUCA karin lokacin aiki a jamhuriyar tsakiyar Afirka (CAR), zuwa 31 ga watan Janairun shekarar 2014.

Kudurin na nunin cewa, kwamitin sulhun da ya kunshi kasashe 15, ya yi kiran hanzarta aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Gwamnati da 'yan kungiyar gamayya ta Seleka da kuma yarjejeniyar siyasa ta warware rikicin.

Sakamakon wannan karin lokaci, kasar za ta samu damar mai da hankali kan tabbatar da doka da oda, sa kaimi kan harkokin tsaro, da kuma kare jama'a fararen hula har ma da 'yan kasashen waje, kana za ta yi aiki da abokanta wajen kara ingancin dakarun kasar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China