Kodegue ya ce, akwai 'yan kungiyar LRA kimanin 1250 da ke yankin gabashin kasar Afrika ta tsakiya da suka amince da kawance damara, cikinsu har da wasu mata da yara. Wadannan dakaru na LRA suna lardin Bria, inda ake kidayar yawan mutane da makamai.
A birnin Libreville hedkwatar Gabon, wani jami'in M.D.D. da ke yankin tsakiyar Afrika ya bayyana cewa, gwamnatin Afrika ta tsakiya ta riga ta mika rahoto ga M.D.D. cewa, akwai dimbin 'yan kungiyar LRA da ke kasar da suka amince da kwance damara, kuma M.D.D. na shirin tura wasu ma'aikata zuwa wannan yankin.
An kafa kungiyar LRA a karshen shekaru 80 na karnin da ya gabata, tare da janyo taba tada zaune tsaye a yankin arewacin kasar Uganda, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu goma, tare da haddasa miliyoyin mutane barin gidajensu. Bayan da sojojin kasar Uganda suka tarwatsa su, 'yan kungiyar sun yi tsira zuwa kasar Sudan ta Kudu, yankin arewa maso gabashin kasar Kongo(kinshasa), da Afrika ta tsakiya.(Bako)