Bisa kiyashi da MDD da ma wasu hukumomi masu zaman kansu suka yi, an ce, tun lokacin da aka dakatar da aikin ciniki daga watan Disamba na shekarar bara tsakanin yankin da kungiyar adawa ta Seleka ta mallaka da sauran wurare, aka samu hauhawar farashi, bisa kalaman kakakin MDD Martin Nesirky yayin taron manema labaru a wannan rana.
WFP ta nuna cewa, kwasar ganima da aka yi a wannan wuri ya haddasa koma baya waje samar da kayayyaki, da kuma abinci, da ma wasu kayayyakin gona da dabbobi, ga kuma fargaba da manoma ke yi inda hakan ya hana su gudanar da aikinsu.
Bugu da kari WFP ta ce, yawan abinci da ake bukata ya karu da kashi 40 bisa dari a wurare dake karkashin sojin kasar. Amma, a cewar Nesirky, wasu wuraren dake karkashin Seleka na fama da karancin abinci saboda hauhawar farashin, inda hakan ya kawo illa ga mutane fiye da dubu 800 a wadannan wurare. (Amina)