Ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, ya bayyana a ran 17 ga wata a birnin Paris cewa, Faransa za ta ba da taimako ga Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, wajen tabbatar da doka da oda, muddin kasar ta kafa sabuwar gwamnati bisa doka.
A wannan rana, a gun taron majalissar wakilan kasar, Laurent Fabius ya ba da jawabi cewa, Faransa na goyon bayan duk wani kokarin da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya zata yi, wajen maido da zaman karko a kasar, amma dole ne ta kafa sabuwar gwamnati bisa doka wadda kuma aka amince da ita. Amma ya zuwa yanzu, ba a kafa irin wannan gwamnati ba tukuna. A wani labarin mai alaka da wannan kuma, kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika ECCAS ta kira taron musamman na shugabanninta a birnin N'Djamena, hedkwatar kasar Chadi a ran 18 ga wata, domin tattaunawa kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya. (Amina)